Featured
Hafsat Ganduje Ta Kaiwa Dahiru Mangal Ziyarar Ta’aziyyar Mahaifiyarsa
Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje Uwar gidan Gwamnan jihar Kano ta kai ziyarar ta’aziyya ga fitaccen attajiri Alhaji Dahiru Bara’u Mangal a Katsina Bisa rasuwar Mahaifiyarsa Hajiya Murjanatu.
KakakiHausa ta rawaito cewa Hajiya Murjanatu ta rasu ta bar ‘ya’ya biyu Alhaji Dahiru Mangal da Alhaji Bashir Mangal.
A yayin ziyarar ta’aziyya, farfesa Hafsa Ganduje ta sami tarba daga mai dakin gwamnan jihar Katsina Hajiya Hadiza Aminu Ballo Masari, inda suka garzaya gidan Mangal domin yin ta’aziyya.
Hafsa Ganduje ta nuna alhininta matuka da rasuwar murgayya Hajiya Murjanatu, yayin da ta yi fatan samun rahama a gareta da sauran al’ummar Musulmi baki daya.
