Labarai
Matashi ya hallaka abokinsa ta hanyar caccaka masa Almakashi a Kano
Rundunar ƴan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi Yusuf Gambo mai shekaru 19 da ya caccakawa abokinsa Almakashi, abinda yayi sanadiyyar mutuwarsa har lahira.
Yusuf ya kashe abokinsa mai suna Usman Rabi’u Abubakar bayan sun Haura gidan Zoo da ke birnin Kano domin yin shaye-shaye, amma sai hatsaniya ta kaure tsakaninsu.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda na Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da labarai faruwar lamarin, inda ya ce za su miƙa wanda ake zargi gaban kotu da zarar sun kammala bincike.
