Connect with us

Featured

Fagen Wasanni: Babu ƙabilanci a ƙungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya

(1) Ni ban yarda akwai ƙabilanci a harkar zaɓen ‘yan wasan Super Eagle ba, abin nan zahiri ce idan har mutum ya iya, ya cike duk sharuɗan ɗaukar to babu dalilin da zai sa a ƙi ɗauko shi. Za a ɗauko shi, sai dai a can filin wasan a ƙi sa shi. (ta dalilin rashin discipline ko wani abu – wannan shi da coach ne)

(2) Mutanen Arewa ba su da jajircewa a harkar ƙwallo, asali ma da farko muna yi mata kallon kafirci wanda tuni su ‘yan kudun sun yi mana fintikau a karɓar ta. Sun mayar da ita rayuwarsu.

Idan ka ce an ƙi saka Hausawa ana sa ƴan kudu, kawo mana misalan Hausawan ƙwararru da suka fi waɗanda aka sa ɗin iyawa da jajircewa.

(3) Mu ɗauki misalin tim ɗin mata na ‘Super Falconet’ wacce ‘yar Bahaushe ce ta tafi wani kulob don zama ‘yar ƙwallo?
Yanzu don ba a sa Bahaushiya a Super Falconet har ma ji haushi mu ce ana ƙabilanci?

Akwai abin mamaki mutane ba su duba nakasun da suka haifar ba na makara, ba su yi bibiya ba, ba su yi bincike sun ga yadda ake ɗaukar ‘yan wasa da dalilan ɗaukar su ba, su rinƙa yanke hukunci da ka.

Na yarda ƙabilun Najeriya Yarabawa, Hausawa da Ibo da sauran ƙabilu suna da ƙabilanci, to amma a hurumi irin wannan ya kamata mu rinƙa nazartar ƙabilancin ne, ko wani abu ne ya ratsa, kafin mu yanke hukunci.

Allah Ya kyauta.

Kabiru Yusuf Fagge, ya rubuto daga Kano

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet