Connect with us

Labarai

Rikicin APC A Kano: Ko kashi ɗaya ba za mu baiwa ɓangaren Ganduje ba – G7

Ɓangaren tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya yi ikirarin cewa ba zai janye ƙarar da ke gaban kotun daukaka ƙara ba har sai an tabbatar masa da shugabancin jam’iyyar APC a matakin jiha kuma ko kashi ɗaya na shugabancin jami’yyar ba za su baiwa ɓangaren gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba.

Jawabin hakan ya fito daga bakin Kwamared Alhassan Uba Idris a lokacin da ya ke tattaunawa da sashen Hausa na BBC a yau Laraba.

“Ba za mu yarda mu janye maganarmu daga kotu ba, sai an tabbatar jam’iyya tamu ce, shugabanci namu ne, sannan za mu je babban taron jam’iyya mun dawo, mun zauna daram dam mun buɗe sakatariya, Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya ci gaba da shugabancin jam’iyya shi ne za mu yarda da wani abu, bayan wannan babu komai”.

Alhassan Uba wanda tsohon ɗan majalisar wakilai kuma jigo a tsagin Malam Ibrahim Shekarau da su ke biyayya ga Alhaji Ahmadu Haruna Zago, ya ƙara da cewa tayin da kwamitin sulhu ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ya yi na rabon muƙamai ba abu ne mai yiwuwa ba.

“Tayin da aka yi cewa a raba jami’iyya 50-50, mu kuma yanzu da jam’iyya ke hannunmu ba wanda za mu bai wa kashi 50, ko kashi 1 ba za mu bayar ba”.

Har yanzu dai an kasa cimma matsaya a sulhun da uwar jam’iyyar APC ke ƙoƙarin yi tsakanin ɓangaren gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet