Labarai
Biodun Oyebanji Ya Zama Dan Takarar Gwamna A Jam’iyyar APC A Jihar Ekiti
Tsohon sakataren gwamnatin jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya zama dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC a jihar Ekiti.
Mista Oyebanji ya samu nasara ne da kuri’u 101,703, inda ya doke sauran ‘yan takara bakwai.
Takaddar kuri’u ya nuna cewa Bamidele Faparusi ya samu kuri’u 376, Ojo Kayode ya samu kuri’u 767, Opeyemi Bamidele, Sanata mai ci 760, Dayo Adeyeye, tsohon dan majalisa ya samu kuri’u 691, Femi Bamisile ya samu kuri’u 400,.
Sauran sun hada da Toyin Afolabi wanda ya samu kuri’u 47 da Demola Popoola wanda ya samu kuri’u 239.
Tun da farko dai ‘yan takara bakwai ne suka sanar da janyewarsu daga takarar, bisa dalilan da suka sa aka samu kura-kurai.
