Connect with us

Labarai

Shugaban Kwamitin Zaɓen Fidda Gwani Gwamna Badaru Ya Mika Rahotonsa

Gwamnan jihar Jigawa Alh. Mohammed Badaru Abubakar a ranar Juma’a ya mika rahoton zaben fidda gwani na jam’iyyar (APC) na jihar Ekiti.

Gwamna Badaru shi ne shugaban kwamitin APC mai mutane bakwai da suka gudanar da zaben fidda gwani na farko a ranar Alhamis 27 ga watan Janairu, 2022.

Daraktan jam’iyyar na APC, Farfesa Ussiju Medaner ne ya karbi rahoton a madadin kwamitin tsare-tsare na riko CECPC a sakatariyar jam’iyyar ta kasa, a Abuja.

Da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon zaben fidda gwanin, Gwamna Badaru ya ce: “Mun mika takardun sakamako da rahotanni inda aka gudanar da zabe – 166. An hargitsa unguwanni 11 kuma mun soke wuraren. Amma a cikin gundumomi 166, mutane sun taka rawa sosai. Kuma ina tsammanin ku duka kuna da bidiyon abun da ya faru a cikin dukkan gundumomi 166 ban da gundumomi 11.

“Kwamitin ya sauka ne a ranar 26 ga watan. Na yi taro da dukkan masu son tsayawa takara, 7 sun halarta a cikin 8. Kuma mun tattauna ka’idojin kuma mun amince da dukkan sharuddan,” Gwamna Badaru ya kara da cewa.

Ya yi kira ga masu neman takara da su marawa jam’iyyar baya da kuma dan takarar da ya lashe zaben gwamna da za a yi a jihar Ekiti.

“Su (masu takara) ’yan jam’iyya ne. Abin da muke sa ran za su yi shi ne su hada kai da mu don mu cigaba da gina jam’iyyar mu kuma mu cigaba da mara wa dan takarar da ya fito baya.

“A wajen bude huldata da masu son tsayawa takara, a taron masu ruwa da tsaki da muka gudanar a jihar Ekiti, na shaida musu cewa mulki daga wurin Allah yake. Kuma Allah ne kadai yasan wanda zai yi nasara”. Gwamna Badaru ya bayyana.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvmarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasibomcasibomjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasibomgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet