Connect with us

Labarai

EFCC ta tsare Darakta-Janar na VON, Osita Okechukwu, bisa zargin almundahana

Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Zagon-ƙasa, EFCC, ta tsare Darakta-Janar na gidan rediyon ƙasa, Voice Of Nigeria, VON, Osita Okechukwu.

Wata majiya da ke kusa da hukumar ta bayyana cewa an tsare Okechukwu ne bisa zargin haɗin-baki, ɓata sunan ofishi da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma da su ka kai Naira biliyan 1.3.

Majiyar ta ƙara da cewa Darakta-Janar ɗin ya isa shelkwatar EFCC da ke Abuja da misalin karfe 1:30 na rana domin amsa gaiyatar da ta yi masa.

Majiyar ta baiyana cewa har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, Okechukwu yana hannun hukumar EFCC.

“Har yanzu yana tare da jami’an EFCC.”

Da aka tuntubi mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya tabbatar da gaiyatar shugaban VON ɗin, amma bai ƙara cewa komai ba bayan wannan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet