Connect with us

Labarai

Kungiyar Tarayyar Afrika AU Ta Dakatar Da Kasar Burkina Faso Da Kungiyar

Kungiyar Tarayyar Afirka ta ce a yau litinin ta dakatar da Burkina Faso a matsayin martani ga juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Roch Marc Christian Kabore a ranar 24 ga watan Janairu.

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar su 15 ya fada a shafinsa na Twitter ya kada kuri’ar “dakatar da #BurkinaFaso a dukkan ayyukan kungiyar ta AU har sai an dawo da tsarin mulkin kasar yadda ya kamata”.

Tuni dai Moussa Faki Mahamat, shugaban hukumar Tarayyar Afirka ya yi Allah wadai da juyin mulkin a ranar da abin ya faru kuma kafin a bayyana ko wane ne ke daukar nauyin.

Kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka ta dakatar da Burkina Faso a ranar Juma’a tare da aikewa da tawaga domin ganawa da gwamnatin mulkin soji ranar Asabar.

Juyin mulkin dai shi ne tashin hankali na baya-bayan nan da ya afku a Burkina Faso, kasar da ba ta da makama, wadda ta yi fama da tashe tashen hankula tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a shekara ta 1960.

Rikicin masu ikirarin jijadi da ya bazu kan iyakar kasar Mali ya kashe mutane sama da 2,000 tare da tilasta wa wasu miliyan 1.5 barin gidajensu tun daga shekarar 2015.

Mali da Guinea su ma a yammacin Afirka an yi juyin mulki cikin watanni 18 da suka gabata wanda ya sa kungiyar ta AU ta dakatar da su.

An kuma dakatar da Sudan bayan juyin mulkin da aka yi a watan Oktoba. Jami’an diflomasiyya sun ce ana sa ran za a tattauna batun juyin mulki a babban taron kungiyar AU da za a yi a Addis Ababa a karshen mako.

AFP

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet