Labarai
Abun Da Yasa Gwamna Ganduje Bai Halarci Wajen Taron Sulhun Jam’iyyar APC Ba
Shugaban jam’iyyar (APC) tsagin gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya ce rashin zuwan gwamna Abdullahi Umar Ganduje wajen taron sulhu na jam’iyyar ba da gangan ba ne.
Abbas ya shaidawa Daily Telescope a ranar Talata cewa, wasu muhimman ayyuka a jihar Kano ne suka shagaltar da Ganduje.
Cigaban ya tabbatar da labarin Solacebase a ranar Talata kan rashin halartar Gwamna Abdullahi Ganduje a taron zaman sulhu sau biyu.
Ya ce: “Kowa ya sani cewa a yau, Talata, gwamnan ya karbi bakuncin wasu muhimman mutane a jihar domin bikin kaddamar da kamfanin shinkafa na Gerawa a hukumance.
“Gwamnan babban bankin kasa, Mista Godwin Emefele, gwamnan jihar Kebbi takwaransa na Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar duk sun hallara a Kano yau domin kaddamar da kamfanin shinkafa na Gerawa.
Ya ce ba za a yi adalci ba gwamnan ya yi watsi da wannan muhimmin taron domin halartar taron.
“Hakika taron yana da mahimmaci ga gwamna, amma a bayyane yake cewa kaddamar da kamfanin shinkafa ya wuce taron. Wannan wani abu ne da zai kawo dama ga matasanmu masu tasowa, ba shakka, ba za ku iya kwatanta shi da taron siyasa ba.
“Duk da haka, yayin da muke cigaba da cewa, a shirye muke don yin sulhu na gaskiya, na tabbata gwamna zai ci gajiyar wannan muhimmin taro. A shirye yake ya sasanta da bangaren Shekarau na APC.”
