Labarai
An Kara Adadin Yawan Matan Da Ake Tantancewa Kan Cutar Sankarar Mahaifa A Jihar Kebbi
Gwamnatin jihar Kebbi ta kara yawan mata masu zuwa tantance cutar sankarar mahaifa daga dubu biyar zuwa dubu talatin da biyar a jihar.
Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya ba da izinin baiwa mata da dama damar yin gwajin domin karfafa yaki da cutar daji da wuri.
Ya ce ciwon sankarar mahaifa yana da muni kuma yana bukatar daukar mataki cikin gaggawa, da gangan da kuma yanke hukunci, domin rigakafi da shawo kan mata.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki, gwamnan ya ce ya yi amanna cewa ana iya rigakafin cutar kansa kuma gano shi da wuri yana sa a samu saukin magani.
Sanarwar ta kuma ruwaito kwamishinan lafiya na jihar Jafar Muhammad yana mai cewa gwamnan ya kuma amince da samar da kwararrun mashawarta domin tabbatar da nasarar shirin.

Ya ce, tuni aka horas da ma’aikatan lafiya dari a fadin jihar domin saukaka gudanar da shirin.
Ya kuma yi kira ga daukacin matan jihar da su ci gajiyar shirin da nufin sanin matsayinsu.
Ya kuma yi kira ga shugabannin gargajiya da na addini da su wayar da kan ‘yan kasa musamman mata wajen ba da himma kan aikin tantancewa da jinya kyauta da shirin ya samar .
