Connect with us

Labarai

An Kashe Mutane Uku A Harbe-harbe Biyu A Wasu Makarantun Amurka

An harbe jami’an ‘yan sanda har lahira a harabar wata kwaleji da ke jihar Virginia ta Amurka a ranar Talata, yayin da wani dalibi ya mutu, daya kuma ya samu rauni a wani harbi da aka yi a wata makaranta a jihar Minnesota a ranar.

An harbe jami’ai biyu, jami’in tsaro na kwalejin da kuma jami’in tsaro na doka a harabar, kafin wanda ake zargin ya tsere daga wurin a kwalejin da ke Virginia, a cikin wata sanarwa da ‘yan sandan jihar Virginia suka fitar ta shafin Twitter.

Jami’an tsaro da dama sun isa harabar kwalejin Bridgewater da misalin karfe 1:20 na rana (1820 GMT) domin mayar da martani ga rahotannin harbe-harbe, a cewar sanarwar, wacce makarantar kuma ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

Wanda ake zargin, dan shekara 27 mai suna Alexander Wyatt Campbell, daga baya an kama shi, in ji ‘yan sandan jihar Virginia, inda ya kara da cewa ya samu “rauni da ba zai yi barazana ga rayuwa ba.”

Har yanzu ba a bayyana ko ‘yan sanda ne suka harbe shi ba ko kuma raunin da kansa ya yi. Tuni dai aka tuhume shi da laifin kisan kai, in ji ‘yan sanda.

Garin Bridgewater, da ke da nisan kimanin sa’o’i biyu da rabi kudu da babban birnin kasar Amurka na Washington, kuma inda kwalejin Bridgewater , ya aike da sanarwar da misalin karfe 1:30 na rana, inda ya yi gargadin cewa wani dan bindiga ya kai hari, in ji kafofin watsa labarai na kasar.

Makarantar ta fitar da sanarwar karara a yanar gizon ta da misalin karfe 4:30 na yamma.

Wata daliba, mai shekaru 21, Kasey Truslow, ta shaidawa jaridar Washington Post cewa ta ji karar harbin bindiga a wajen tagar wani ginin ajujuwa.

“Bayan harbi na biyu, mun hau kasa. Mun zauna a kasa na awa daya,” inji ta.

Gwamnan Virginia Glen Youngkin ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, “An sanar da ni halin da ake ciki a Kwalejin Bridgewater. Wanda ya yi harbin yana tsare kuma ‘yan sandan jihar da na yankin suna wurin.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahisjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet