Labarai
Tsohon Gwamnan Jigawa Ya Ce Zai Goyi Bayan Duk Dan Takarar Da Yafi Dacewa A 2023
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce zai goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa da ya fi dacewa da kasar nan a 2023.
Lamido, wanda ya yi magana daga jihar Kano a ranar Laraba, ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Channels ta cikin shirin Politics Today.
“Barin mu nemo irin mutumin da zai kasance tare da Najeriya ga dukkan ‘yan Najeriya,” in ji shi. “A gare ni, duk inda ya fito, duk wanda zai yi wa Najeriya hidima shi ne zan ba shi goyon baya.”
Da aka tambaye shi ko jiga-jigan Arewa sun yanke shawarar cewa yankin ya samar da shugaban kasa, tsohon gwamnan bai amsa mai kyau ko mara kyau ba.
Maimakon haka, ya ce bai yarda da haɗin kai na yanki ko kabilanci ba.
Lamido, jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana damuwarsa kan yadda duk kokarin da aka yi a baya na tabbatar da zaman lafiya a kasar nan ya ci tura a ‘yan kwanakin nan sakamakon karuwar kabilanci da addini.
A cewar sa, ana bukatar a sauya irin wadannan abubuwa, sannan kuma Najeriya na bukatar hazikan shugabanni masu nagarta da za a zaba a matsayin shugaban kasa da kuma rike wasu muhimman mukamai a kasar.
Da yake mayar da martani kan sanarwar da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya yi a baya-bayan nan na shiga fafatukar neman ganin ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023, tsohon gwamnan ya yi imanin cewa tsohon na daya daga cikin wadanda suka cancanta.
Ya bayyana cewa gwamnan ya ziyarce shi kwanan nan, yana mai jaddada cewa yana da kwarewa da kuma ilimin da ake bukata don zama shugaban Najeriya.
