Labarai
Jam’iyyar PDP Ta Yi Gargaɗi Kan Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara
Jam’iyyar PDP ta yi gargadi kan matakin da majalisar dokokin jihar Zamfara ta dauka na tsige mataimakin gwamnan jihar Mahdi Gusau.
A wata sanarwa a ranar Asabar ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, ta bayyana matakin a matsayin wanda ya sabawa doka kuma ya sabawa tsarin demokradiyya.
Jam’iyyar PDP ta kuma zargi gwamnan jihar Bello Matawalle da yin amfani da ‘yan majalisar wajen yin irin wannan yunkuri, inda suka yi yunkurin haddasa rikici a jihar.
“Wannan tsarin tsigewar ba bisa ka’ida ba, duk da umarnin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar mai lamba FHC/ABJ/CS/ 650/2021 yana nuna babban tasiri ga zaman lafiya da tsaro ba a jihar Zamfara kadai ba, har ma da yankin arewa maso yamma baki daya, da kuma ci gaba da dorewar dimokradiyya a kasarmu,” in ji sanarwar.
“A bayyane yake cewa wannan firgicin da Gwamna Matawalle ya yi ya samo asali ne sakamakon fahimtar da ya yi cewa wa’adin mulkin PDP da ya sace ya koma APC yana gab da kwatowa ta hanyar tsarin shari’a na kotu da mayar da shi ga mataimakin gwamna; shi (Matawalle), kasancewar ya saba wa tanadin kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya yi rikon sakainar kashi ya koma APC lokacin da babu wata baraka a PDP.”
