Connect with us

Ilimi

Kalaman Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya sun tayar da ƙura

Kalaman da fitaccen malamin addinin Musluncin nan Dakta Abdallah Usman Kaya ya yi akan ma’aikatan jinya sun tayar da ƙura tare da haifar da zazzafar muhawara a tsakankanin ƴan Najeriya.

Tun da farko Shehin Malamin ya yi zargin cewa masu aikin jinya da ke asibitoci a jihar Kano suna ƙetare ƙa’idojin aikin su tare da dangan ta su da abin da bai kamata ba a lokacin da su ke aikin kwana.

Malamin ya yi wannan zargin ne a wani shiri da ake gabatarwa a gidan Talabijin na Africa TV inda ya ce malaman jinyar ba sa la’akari da jinsi a lokacin da su ke gudanar da aikin su. Domin su kan cakuɗu a daki ɗaya duk kasancewar su ba muharraman juna ba.

“A asibitocinmu, akan umarci ma’aikatan jinya maza da mata da su yi amfani da ɗaki ɗaya, sannan kuma su kan rufe kansu a cikin ɗakin a wajejan ƙarfe 3 na dare”.

“Wannan yana zuwa ne a dai-dai lokacin da mazajensu su ke kwance a gida tare da tunanin matansu suna aiki a asbiti. Sai dai kuma komai zai iya faruwa”.

Haka kuma Shehin Malamin ya bayar da misalin yadda wata mata mai kimanin shekaru 50 a duniya ta bar aikinta a ɗaya daga cikin asibitocin wanna jiha sakamakon matsin lamba daga wurin abokin aikin ta.

Ya ce “Idan har hakan zai faru akan ma’aikaciyar jinya ƴar shekara 50, mai ku ke tunani akan yaran da suka kammala karatu da ba su gaza shekaru 30 ba?”.

Martanin Kungiyar Ma’aikatan Jinya

Sai dai a wata tattaunawa da jaridar SAHELIAN TIMES, da shugaban ƙungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma reshen jihar Kano, Kwamared Ibrahim Maikarfi Muhammad, ya ƙalubalanci iƙirarin malamin kan wannan batu.

Muhammad ya kuma nemi malamin da ya janye kalaman sa kan ma’aikatan jinyar ko kuma samar da rashin yarda tsakanin ma’auratan.

Shugaban ya yi ƙarin haske da cewa ”Babu inda za ka samu ma’aikaciyar jinya da shekarunta suka kai 50 tana aikin dare duba da cewa shekarunta na aiki sun kusa ƙarewa”.

Me Shehin Malamin Ya Ce?

Sai dai Shehin Malamin ya janye kalaman zargin aikata baɗalar ga Malaman jinya din. Ya ce rashin fahimta ne ya sanya yayi kalaman zargin baɗala tsakanin ma’aikatan jinya, sai dai yace tuni sun fahimci juna tsakaninsa da ma’aikatan jinyar na Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet