Connect with us

Featured

Duk masu faɗa da Abdallah Usman Gadon Ƙaya wa’azi ne bai dame su

Mallam Abdullahi Gadon Kaya da sauran ƴan uwa masu wa’azi, ku ɗauki haƙuri. Aksarin masu faɗa da ku ba wai neman gaskiya ne ya dame su ba; wa’azin ne ba su so.

Yau idan da za ka yi wa’azi a kan sallar dare ka kwaɗaitar ka kawo ayoyi da hadisai, kada ka yi mamaki idan wasu suka tafi suna yaɗa cewa ka ce dukkan wanda ba ya sallar dare kafiri ne.

Yanzu dukkan abin da ake cece kuce a kansa shi ne maganar kura – kurai da akan samu daga ɓangaren wasu masu aikin asibiti. An ce Mallam Abdullahi ya ce ma’aikatan asibiti (Nurses, Doctors, Midwives) mazinata ne. Duk da ban saurari wannan ɗanuwa ba na san ƙarya ake masa, domin babu wani mai alaƙa da ilimin addini da zai yi wa jama’a masu yawa (waɗanda akwai mutanen kirkin da suka shahara da nagarta a cikinsu) kudin goro ya jefe su da zina.

Ba abin mamaki ba ne ka ga mutumin da a ma’aunin boko masani ne amma idan ya tabka maka wata katobarar a addini ko kare ba ya ci. Dazu na karanta rubutun wani babban mutum yana magana a kan wani limami da ya yi huduba a kan zina da a kan samu wasu matan aure na yi a jami’ah. Shi a fahimtar sa tun da limamin yayi huduba a kan wannan mas’alar to yana nufin duk macen auren da ke karatu a jami’ah mazinaciya ce. Wannan yana nuna jahiltar manufar wa’azi da uslubin Alkur’ani da Sunnar Manzo alaihis salatu was salaam.

Zan bada misali guda. Akan kuskure daya da wani Sahabi (Hatib bn Abi Balta’a) yayi a lokacin da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) yake shirin tafiya Makka da yaki, ayoyin farko na suratul Mumtahana suka sauka. Tare da kausasawa da wadannan ayoyi suka yi a kan kuskuren Hatib da cewa ba su ambaci sunansa ba, babu wani Sahabin da ya fahimci cewa an yi wa sahabbai kudin goro ne. Akwai misalai da yawa irin wadannan a Alkur’ani da Sunna. Musulunci addini ne da ke kare mutuncin jama’a. Shi ya sa idan Manzon Allah (SAW) ya ga wani yana kuskure ba ya fallasa shi a cikin mutane, sai dai yayi jirwaye. Misali ya kan ce, “Mi ya sa wadansu daga cikinmu su kan yi abu kaza da abu kaza?” duk da cewa mutum daya ne ko biyu suka yi shi.

Su kuma ‘yan “Comrade” mutane ne marasa hikima. So su ke a rinka kiran sunayen mutane ana zagi a kan mumbari domin wai a nuna ana da hujja.

A karshe ina zarginmu, mu da mallaman mu domin rashin bullo da sabbin hanyoyi na jawo irin wadanda mu kan kira ‘yan boko aƙida a jiki. Har yanzu hanyar mu ta wa’azi ba ta wuce muyi karatu a masallaci ba ko a radio ko TV waɗanda duk wanda bai je ba ko ya buɗe ya saurara bai san mi muke fada ba. Sai dai idan masu neman ɓata karatun sun yanko magana sun kawo masa ya hau ya zauna a kai.

Prof Abdussamad Umar Jibia, malami ne a jami’ar Bayero da ke Kano

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet