Kasuwanci
Yadda za ku samu jarin da Gidauniyar Sana’a Da Ilimi za ta baiwa mata a Kano
A cigaba da shirye-shiryen bukukuwan ranar Mata ta duniya da ake a duk ranar 8 ga watan Maris domin nazari kan ci gaba da kuma kalubalen da suke fuskanta, gidauniyar Sana’a da Ilmi ta fitar da sanarwar wata ƙwarya – ƙwaryar gasa a tsakanin mata ƴan asalin jihar Kano da su ke yin wata sana’a kuma ba su wuce shekaru Talatin da haihuwa ba.
Shugabar gidanauniyar ta Sana’a da Ilimi Hajiya Amina Ado ce ta sanar da hakan ne a shafinta na LinkedIn da kuma shafinta na Twitter. Inda ta ce gidauniyar ta ware kimanin Naira Dubu Ɗari Uku (300,000) domin rabawa mata guda uku da su ka yi nasarar lashe gasar.
Ga Matakan Za A Bi Wajen Samun Dacewa Da Tallafin Gidauniyar Ta Sana’a Da Ilimi:
– Ya zama wajibi duk macen da ta za ta nema ta kasance tana da wani kasuwanci ta ke yi tare da gabatar da shaidar hakan.
– Bayanin yadda za ki yi amfani da tallafin kuma kar su gaza kalmomi 500.
– Samar da shaidar da za ta tabbatar da cewa macen da za ta nemi tallafin ba ta wuce shekaru 30 da haihuwa ba.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa za a iya tura bayanan ta adireshin imail kamar haka: sanaadailmi@gmail.com a ranar 2 ga watan Maris.
A ƙarshe sanarwar ta ce ranar 8 ga watan Maris za a sanar da wadanda su ka yi nasara, inda aka ware kimanin Naira Dubu Ɗari Uku (300,000) da za a rabawa mata ukun da su ka yi nasara, inda kowacce mace za ta samu Naira Dubu Ɗari (100,000).
