Uncategorized
Ana zalunci a masana’antar Kannywood – Naziru Sarkin Waƙa
Fitaccen mawakin Hausa, Naziru M Ahmad, wanda a ke yi wa laƙabi da Sarkin Waƙa, ya ce galibin masu shirya fina-finan Hausa azzalumai ne da ke tauye hakkin wadanda ke aiki a karshinsu.
Ahmad ya baiyana hakan ne a matsayin martani a kan maganar da shahararriyar ƴar wasan Hausa, Ladi Chima, wacce a ka fi sani da Tambaya ta fada a wata ganawa da ta yi da BBC Hausa, inda ta ke cewa naira dubu 2 zuwa 3 a ke biyan ta idan ta yi fim.
Wannan maganar ta tada ƙura a masana’antar Kannywood, inda wasu fitattun ƴan fim, kamar su Ali Nuhu, su ka fito su ka maida nata da raddi.
Da ya ke nashi tsokaci a kan batun, Sarkin Waƙa ya baiyana a wani faifan bidiyo da ya wallafa mai mintuna shida ranar Alhamis yana kalubalantar ‘yan fim din Hausa.
Sarkin Waka ya baiwa Tambaya kariya inda ya bayyana irin cin zalin da ‘yan fim din ke yiwa wadanda ake sakawa a fim.
A cewar Ahmad, babu ƙarya a cikin kalaman da Ladi Chima ta faɗa kuma bai kamata a fito a yi mata irin wannan cin zarafi ba.
“Na taba Kiran wata dattijuwa Aikin fim Bayan ta gama na dauki kudi na bata kawai sai matar nan ta rikice tana yimin godiya kamar ta yimin sujjada , sai na tambaya ya haka sai aka ce ai dubu biyu Dubu uku ake basu, yau kuma ta ji Dubu 10 a hannunta shi yasa ta rikice”. Inii Nazir M Ahmad.
Sarkin Waka ya ce wasu matan ma sai anyi lalata da su sanan ake sanyasu a cikin fim, yayin da wasu ma su ke biyan kudin dan sanya su.
“Duk da bana harkar fim sosai amma nasan maganar Ladin Cima gaskiya ce, sannan muna sane da yadda wasu ma maimakon a biyasu idan an saka su a fim sai dai su su biya.
“Wasu kuma yan matan ayi lalata dasu kafin a saka su a fim, wannan Kowa ya sani”. Inji Sarkin waka
Naziru ya kara da cewa masana’antar tana samun nakasu, kuma ya kalubalanci duk wadanda suka karyata zancen dattijuwar da cewar su yi rantsuwa kan abunda da ta fada ba gaskiya ba ne.
Naziru ya kalubalanci Ali Nuhu da Falalu A Dorayi bisa take gaskiya kan furucin su, inda ya ce ya kalubalance su su fito su musanta zancensa idan ba gaskiya ya fadaba.
Sai dai shi ma a safiyar Juma’ar nan mai Shirya fina-finan Hausa nan Abubakar Bashir Mai shadda ya mayar masa da martani tare da Karyata dukkanin kalaman Nazirun.
