Featured
Ko Ƴan Kannywood za su gurfanar da Naziru Sarkin Waƙa kan ɓata suna?
Maganar Mawaki Naziru M Ahmad cewa akwai da yawan ƴan mata waɗanda sai an yi zina da su ake saka su a fim gaskiya ce. Na ga har rantsuwa ya yi kan maganar tasa bari mu jira cikin ƴan fim ko za a sami masu mazantakar da zai fito ya rantse cewa bai taɓa lalata da mace kafin ya saka ta cikin fim dinsa ba. Za ku gani wallahi ba za su rantse ba domin aikinsu ne lalata yaran mutane, idan ƙarya Naziru ya yi muku to ku kai shi Kotu kawai.
Ban cika magana kan lamura marasa muhimmanci ba, ban so kuma na yi magana kan Naira 2000 – 3000 da wata tsohuwa ta ce ana biyanta kuɗin aikin fim ba. Amma maganar Naziru ta taɓa min inda ke min ƙaiƙayi.
Na rantse da Allah ƴan matan fim din nan karuwai ne masu lasisi waɗanda ƴan siyasa da masu hannu da shuni ke lalata da su suna ba su maƙudan kuɗaɗe, shi ya sa kuke ganin su suna fita ƙasashen waje suna wadaƙa da kuɗi son ransu, ga zargin neman mata ƴan uwansu da ya mamaye harkar wanda shekarar da ta wuce sai da wata ta tona asirin wata fitacciyar jaruma, ga shaye-shaye da aka shaidi yaran nan mazansu da matansu ke aikatawa.
Su ma mazan da yawansu ba mutanen kirki ba ne, ba su da aiki ban da zinace-zinace da lalata tarbiya. Kuna saka yara mata a fina-finanku kuna zina da su kuna kuma kai su wa ƴan siyasa da masu hannu da shuni ana zina da neman mata ƴan uwansu da su suna ba ku kuɗi. Alhalin kun ƙi saka ƴaƴanku, ƙannenku ko matanku cikin harkar kun killace su a gida. Mu dai ƴan hausa fim ba abin da suka amfana mana ban da lalata tarbiya da ɗabbaƙa shaiɗanci da wanzar da yahudanci. Allah ya sani ina matukar ƙyamar abubuwan da waɗannan mutane ke aikata mana cikin al’ummar mu.
Ban son na kama suna, amma akwai munanan labarai da wani dan fim din ke sanar da ni, wanda na ƙara tabbatarwa cewa yaran nan shaiɗanu ne ko saboda fasikancinsu dole mu yi ta gamuwa da musibu. A haka ne wani ɗan iskan Yaro mai suna Aminu Shariff Momo ke cewa wai da a gina masallaci da Islamiyya gwara a yi film. Ke nan yana nufin da a dinga sallah ana koyawa yara tarbiyya da karatun Alqur’ani gwara a dinga assasa karuwanci, ma*digo, zinace-zinace da shaye-shaye a Kano.
Ko watanni biyu da suka wuce an samu wani Sanata a Kano mai suna Barau I. Jibrin inda ya tara waɗannan ashararun yara ya kashe musu kusan miliyan dubu ɗaya, wanda a sannan ne mutane ke mutuwa saboda rashin kudi a Asibiti wasu na mutuwa saboda yunwa, a lokacin ne na yi rubutu har aka sami wani mutum mai suna Hamisu Iyantama ya fito yana min barazanar lallai na janye kalamaina, abin da ban yi ba ke nan. Sai dai tarihi ba zai manta da ɓarnar da su Iyantama suka yi wa al’umma ba. A shekarun baya ne Yahudawan Amurka suka ba wa Hamisu Iyantama kwangilar shirya fim na ɓatanci ga addini da tarbiyya wanda gwamnatin Malam Shekarau ƙarƙashin hukumar tace fina-finai wacce Abubakar Rabo Abdulkarim ke jagoranta ta kwamushe Iyantama zuwa Kurkuku, amma Amurka ta shiga ta fita aka sake shi. Mutum mai mummunan tarihi irin wannan ne zai dinga barazana saboda wani Sanata mai suna Barau Jibril wanda ya butulcewa maigirma Gwamna Ganduje Khadimul Islami.
Da yawan yaran nan ƴan fim ashararu sun yaƙii Gwamna Ganduje lokacin zaɓe, saboda gwamnatinsa na ɗaukan matakin magance ɓata tarbiyyar da suke yi ƙarƙashin hukumar Hisba da hukumar tace fina-finai.
Allah Ya Shiryi Wadannan Yara Idan Ba Za Su Shiryu Ba Ya Yi Musu Abin Da Suka Cancanta Da Shi.
Indabawa Aliyu Imam ya rubuto daga Kano – Najeriya
