Connect with us

Featured

Alhaji Halilu Ahmed Getso: Gwani Na A Duniyar Aikin Rediyo

A lokacin da ake bikin ranar rediyo ta duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin ranar Rediyo ta duniya, ni kuma a lokacin na ke ƙara godewa Allah da ya cikamin burina na zama ɗan jarida wanda hakan ya faru ne sakamakon buɗar da ido da na yi da ita kan ta rediyon a gidanmu.

Kamar yadda ya zama al’adar Bahaushen dauri a wancan zamanin samun akwatin rediyo a kowanne gida a ƙasar Hausa, domin ta nan kaɗai ake samun labarin halin da duniya ke ciki kuma shi Bahaushe mutum ne mai son ya Ilimantu ya kuma nishaɗantu daga wani abu wanda waɗannan abubuwa kaɗan ne daga abubuwan da ake samu daga akwatunan rediyo.

Na taso ni da sauran ƴan uwana mun tarar mahaifiyarmu (Allah ya yi mata rahama), ma’abociyar sauraron Rediyo ce ƙwarai da gaske. Wannan ne matakin farko da ya sanya na fara tunanin su waye haka su ke magana a cikin akwatin rediyo? Kuma nima ya za a yi in zama irinsu?

A wancan zamanin babban gidan rediyon da al’umma su ka fi sauraro shi ne gidan Rediyo Najeriya Kaduna, domin idan ka cire gidan rediyon jihar Kano, to babu wata tashar rediyo ta cikin gida da za a iya kamawa cikin sauƙi. Irin shirye-shiryen da ake gabatarwa a rediyo Najeriya Kaduna kamar su Gatarin Gwari da Jakar Magori da Shafa Labari Shuni da Siyasa Rigar Ƴanci da Wa’azin Musulunci da Duniya Budurwar Wawa da filin Ɗaka da Waje da kuma shirin Wasa Ƙwaƙwalwa, ya yi tasiri ƙwarai da gaske a rayuwata domin ta nan ne na san abubuwa masu ɗimbin yawa!

Na samu kai na da so tare da burin ganin na zama ɗan jarida, kuma hakan yana nasaba da irin soyayya da ƙaunar da na ke yiwa shahararren ɗan jaridar nan kuma gogaggen ma’aikacin Rediyon nan.

Mutum mai fikra da fasaha da kuma balagar iya zance, wato tsohon shugaban gidan Rediyon Najeriya, Kaduna kuma tsohon shugaban gidan Rediyon jihar Kano, Manomi kuma Basarake, Alhaji Halilu Ahmed Getso.

Haƙiƙa wannan bawan Allah ya tasirantu ƙwarai da gaske a zuciyata domin ta kai a dalilinsa na ke ƙaunar duk wani mutumin da ya fito daga garin Getso.

Buhari Abba ya rubuto daga Kano – Najeriya

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet