Connect with us

Labarai

Rikicin APC a Kano: Zamu ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli – G7

Ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau a Jam’iyyar APC a Jihar Kano da ke rikici da tsagin Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya ce shugabancin ɓangaren gwamna ne halastacce.

Shugaban tsagin, Ahmadu Haruna Zago, ƙarƙashin jagorancin Tsohon Gwamna, Sanata Ibrahim Shekarau, ya faɗa wa BBC Hausa cewa za su yi biyayya ga hukuncin amma za su ɗaukaka ƙara.

“Za mu ɗaukaka ƙara mana, ai bin umarnin daban kuma ɗaukaka ƙara daban,” in ji shi.

“Lauyoyinmu na nazari kan hukuncin kotun,” in ji Danzago.

BBC Hausa ta rawaito cewa hakan na nufin Kotun Ƙoli ce za ta raba gardama idan suka ɗaukaka ƙarar, kasancewar Kotun Ɗaukaka Ƙara ce ta yi hukuncin na yanzu.

A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce Babbar Kotun Abuja ba ta da hurumin yin hukunci kan rikicin sannan kuma ta ce shugabancin Abdullahi Abbas ne halastacce – ba na Haruna Zago ba.

A makon da ya gabata ne tsagin Shekarau ya yi watsi da wani yunƙurin sulhu da jam’iyyar ta ƙasa ta yi, inda ta naɗa Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamatin sasanta rikicin da suke yi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet