Labarai
Rikicin APC A Kano: Kotu ta yi watsi da tsagin Malam Shekarau
Kotun ɗaukaka ƙara dake babban birnin tarayya Abuja, ta jingine hukuncin babbar kotun tarayya na warware zaɓen shugabancin mazaɓu na jam’iyyar APC a jihar Kano tsagin gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A zamanta na yau, kotun ɗaukaka karar tace kotun farko bata da ikon yin wannan hukunci, domin batu ne akan rikicin cikin gida na jam’iyyar APC, saboda haka uwar jam’iyyar APC ta ƙasa ce ta ke da alhakin yanke hukunci akai.
