Addini
An zartarwa da wani Namiji da Mace hukuncin Rajamu a ƙasar Afghanistan
Wasu rahotanni daga ƙasar Afghanistan sun bayyana cewa an jefe wani mutum da wata mata bayan da a ka kama su da laifin aikata yi zina a Arewa-maso-Gababshin Lardin Badakhshan da ke ƙasar.
Wasu jami’an gwamnati ne guda biyu na Taliban su ka tabbatar da hakan a yau Laraba. Wani jami’i ya shada cewa an jefe su biyun ne a kotun shari’ar Muslunci.
A Addinin Musulunci, haramcin ne mace da namiji su sadu ba ta da aure ba.
Hakazalika idan namiji mai aure ya yi zina da matar aure kuma a ka samu shaidu huɗu, to hukuncin su shi ne a jefe su har sai sun mutu.
Jami’in ya ce sun amsa laifin su kuma sun ce wajen sau biyu zuwa uku su na saduwa da juna.
Wata jarida ta ƙasar, Hasht-e Subh ta baiyana cewa an jefe su ne a ranar LitininLitinin a bainar jama’a a lardin Nasi.
An ce wani kwamandan Taliban ne ya bayar da umarnin jefe matar da mutumin.
