Connect with us

Labarai

Rikicin APC A Kano: G7 sun nufi kotun koli domin ƙalubalantar nasarar Ganduje

A sakamakon yin watsi da zaben shugaban Jam’iyyar APC ta Kano da kotun daukaka kara ta yi, bangaren Ibrahim Shekarau ya ce uwar Jam’iyya ta yi hanzarin mika takardar shaida ga Abdullahi Abbas domin za su daukaka kara zuwa Kotun Koli.

Wannan turka-turka ta samo asali ne daga zaben shugabanin Jamiyyar APC da aka gudanar a Kano ranar 18 ga watan Oktoban bara, inda aka samu rukuni biyu na shugabanin jam’iyyar APC a jihar.

Rukunin Gwamnan Jihar ta samar da Abdullahi Abbas a matsayin Shugaba, daya rukunin da ke karkashin tsohon Gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau kuma ta samar da Haruna Danzago a matsayin na ta shugaban.

Ganin an samu shugabani biyu, sai bangaren Shekarau ya shigar da kara a kotun tarayya da ke Abuja wajen neman gane wane zabe ne sahihin zabe a jihar Kano a lokacin da aka yi zaben fitar da shugabani.

A ranar 30 ga wata Nuwamba na bara sai kotun tarayya ta yanke hukunci cewa zaben da bangare Shekarau suka yi shi ne sahihi, saboda haka Haruna Danzago shi ne shugaban Jam’iyyar APC a jihar Kano.

Akan haka ne bangaren Gwamna Ganduje ya kai kuka kotun tarrayya cewa su sake duba shari’ar amma aka fatattake su, ganin haka sai suka daukaka kara zuwa kotun daukaka kara ta Abuja inda ta yanke hukunci cewa Abdullahi Abbas na bangaren Ganduje shi ne zababben shugaban jamiyyar APC a Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet