Connect with us

Featured

2023: Yadda Kwankwaso ya ƙaddamar da ƙungiyar ceton Najeriya daga halin wahala

A yau Talata tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya sanar da kafa wata ƙungiya a matsayin ‘Runduna ta Uku’ a babban birnin tarayya Abuja.
Ƙafa wannan ƙungiya na da nasaba da wani yunƙuri na karɓar mulki daga hannun jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2023.

Da yake jawabi a wajen taron, Sanata Kwankwaso, wanda shi ne ya shirya shi, ya ce burinsu shi ne haɗa kai dan ceto kasar nan daga halin da ta tsinci kan ta

“Dukkanmu mun bar gidajen mu domin halartar wannan taro. Rana ce ta musamman a rayuwar al’ummarmu. Rana ta musamman don ceto al’umma.

“Tun da daɗewa ƴan Najeriya suna jiran wannan rana. Abokan ƴan Najeriya da ke waje sun daɗe su na jiran wannan rana kuma lokaci ya yi yau da kuma yanzu.

“A yau, duk al’ummar Najeriya daga kowanne ɓangare da kuma kowacce ƙabila sun taru a nan wajen. Ƙudirinmu ne ganin mun ceto al’ummarmu daga wannan mawuyacin hali.

Tsohon gwamna Kwankwaso ya ce ya gana da abokansa a lokacin kullen korona kuma a ƙarshe sun yanke shawarar cewa dole ne a ɗauki matakin ceto Najeriya.

“Mun yanke shawarar cewa dole ne a fara samun Najeriya kafin siyasa. Yayin da wasu daga cikinmu za su so tsayawa takara, dole ne mu haɗa kai don ceto kasar.

“Kungiyar nan ta mu na da mambobi a kowace karamar hukuma da kuma wajen ƙasar nan” in ji Kwankwaso.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet