Connect with us

Labarai

Jami’an KAROTA sun cafke ɓarawon waya a Kano

Jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta sami nasarar cafke wani matashi mai suna Lawan Khalid, bisa zargin satar wayoyin hannu da kayayyakin jama’a a cikin babur ɗin adaidaita sahu.

Jami’an na KAROTA sun cafke Lawan ɗin ne da misalin ƙarfe 2 na ranar yau Talata, a kan Titin Munduɓawa da ke birnin Kano.

Matuƙin baburin adaidaita sahun mai suna Yahaya Adamu, ya bayyana cewa Lawan ɗin shi da abokansa sun ɗauke shi shata tun daga yankin unguwar Brigade da ke ƙaramar hukumar Nasarawa, inda su ka yi ta walankeluwa da shi a cikin birnin Kano.

Ya ce daga baya ne kuma su ka shiga wani shago inda su ka sato wayoyin mutane.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka shigarwa shago aka ɗebi kaya, Hamza Ichaɓa ya bayyana farin cikinsa, tare da godiya ga hukumar KAROTA kan ƙoƙarin da ta yi wajen kama waɗanda ake zargin.

Hukumar KAROTA ta bayyana cewa nan gaba kaɗan za ta miƙa wanda ake zargin ga rundunar ƴan sanda da zarar ta kammala tattara bayanai a kai.

Dabi’ar ƙwacen waya da lalata ababen hawa da faɗace-faɗacen daba da kuma fashi da makami na ci gaba da ƙamari a Kano

Ko a kwanakin baya ma dai, hukumar ta KAROTA ta cafke wasu da suka cakawa wata mata wuƙa a maƙogwaro, sannan suka sace wayarta.

Sai dai jami’an tsaro na bayyana cewa suna bakin ƙoƙarinsu wajen dakile miyagun ayyuka a birnin Kano da ma jihar baki daya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet