Labarai
Sanata Hassan Nasiha ya zama sabon mataimakin gwamnan Zamfara
Gwamna Muhammad Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya zabi Sanata Hassan Muhammad Nasiha a matsayin sabon mataimakinsa, tare da mika shi gaban Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa.
Hakan ya biyo bayan dawowa daga hutun rabin lokaci da majalisar ta yi, jim kadan bayan tsige tsohon Mataimakin Gwamnan, Mahdi Aliyu Gusau.
Sai dai a zaman Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasiru Muazu Magarya ya karanta wasikar da Gwamna Matawalle wadda ya aike majalisar mai dauke da sunan Sanata Nasiha a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar.
Kafin naɗin sabon Mataimakin Gwamnan shi ke wakiltar shiyyar Zamfara ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawan Najeriya.
A ranar Laraba ce Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta kada kuri’ar tsige Mataimakin Gwamnan Mahdi Aliyu Gusau.
‘Yan majalisa 20 daga cikin 24 ne suka kada kuri’ar goyon bayan tsige Mataimakin Gwamnan, bayan kwamitin da majalisar ta kafa da ke bincike a kan zargin shi da almundahana da kudin gwamnatin jihar ya gabatar da rahotonsa.
Honarabun Magarya ne ya karanta rahoton da kwamitin ya gabatar a ranar Laraba, inda ya tabbatar da cewa lallai Mataimakin Gwamnan ya yi sama da fadi da kudin gwamnatin jihar.
Ko a Talatar da ta gabata Mataimakin Gwamnan ya ki halartar zaman kwamitin mai mambobi bakwai da ke gudanar da ke bincike a kansa.
