Connect with us

Featured

Yaƙin Rasha da Ukraine (I)

Kiris ne ya rage VLADIMIR PUTIN, shugaban kasar Rasha ya karbe kasar Ukuraniya. Tun kusan wata guda kasar Rasha ta jibge sojojinta a duk kan iyakokinta da Ukuraniya. Ta gabas da yamma da kuma ta kudu. Daga shekaran jiya da sojan ruwa dana kasa da sojan sama sun yi wa kasar Ukuraniya kawanya.

Ganin haka, shugaban kasar Ukuraniya ya bada umarnin a fito da bindigogi dubu goma a yi watandar su duk farar hula su diba, a tunkari Rasha. Haka kuma ya yi umarnin duk dan shekara 18 zuwa 60 kada ya fice daga kasar duk rintsi. Shi kansa magajin Garin babban Birnin Ukuraniya Vitali Klistchiko, wanda tsohon dan dambe ne da ministan tsaro za su daura janjami su fito yi taransu.

Dogaron da Rasha take da shi, bai wuce mallakar makamin nukuliya ba. Nukuliya shi yafi kowane makami hadari a duniya. A karfin mallakarsa da yawa babu kasar da ta zarce Rasha. Ita ce lamba daya, sannan Amurka na binta a baya. Rasha ta gaji wannan makamin ne daga tsohuwar rusasshiyar kasar Soveit Union wato USSR. A kasar Ukuraniya ake ajiye da duk nukuliyar Rasha, amma wata yarjejeniya ta shekarar 1994 ta sanya aka maida duk wani makamin na nukuliyar cikin kasar Rasha.

Rasha tana da karfin tattalin arziki, tana cikin manyan kasashen duniya mafi arziki guda takwas G8. Tana cikin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya. Idan ana lissafin mallakar duniya, Amurka ce ta farko, Rasha kuma ta biyu. Rasha ce kishiyar Amurka. Burin Putin shi ne ya rika gogayya da Amurka a kowane fage. In Amurka ta yi gabas, Putin zai yi yamma. Akan samu a wasu loto don wata bukata, su duka biyun su hadu su murkushe wani ko wata da suka shigar musu hanci da kudundune.

Vladimir Putin gagararre ne kuma hatsabibi. Shekararsa 70. Akan mukamin shugabancin Rasha shekararsa 22 kuma ya saita tsarin sai shekarar 2036 zai bar mulki a lokacin ya yi shekara 85. Tsohon soja ne kuma masanin tattalin arziki da ya yi digirin-digirgir. Ya samu shahara da kwarewa a harkar leken asiri har sai da ya rike shugabancin KGB, wato hukumar leken asiri ta tsohuwar Rusasshiyar kasar Soveit Union. Duk wata sabgar tsaro a Rasha ko tsohuwar rusasshiyar Soveit Union da hannunsa. Zaka iya kwatanta shi da aikin DSS ta nan Najeriya ko CIA ta Amurka ko MOSSAD ta Israila ko M15 ta Ingila. Ko ka kwatanta shi da Janar Aliyu Gusau.

Babban abin da yake ciwa Putin tuwo a kwarya shi ne, goyon bayan da Ukuraniya take baiwa Turawa na kasashen yamma da kungiyarsu ta tarayyar Turai wato European Union EU. Kalubale da barazanar da ta fi damunsa kuma shi ne kawancen tsaro na kungiyar NATO. Putin baya son Ukuraniya ta shiga kungiyar NATO, domin in Ukraine ta shiga NATO hakan zai baiwa Amurka damar ta kafa sansanin soja a gurin. Makiyi ya zo kusa da kai, zai ga asirinka kuma zai yi amfani da wannan dama ya cutar da kai, shi ne tunanin Putin. Hanyar da kawai zai bi ita ce ya yi amfani da karfin tsiya ya tunbuke gwamnatin Vlodomyr Zelensky, ya kawo wani karen farauta ya dora. Wannan abu ne mai sauki, saboda karfin Rasha ya nunka na Ukuraniya sau dubu ta kowacce fuska. Kuma sabon fasalin Amurka a karkashin Joe Biden babu shigar da sojin Amurka wani sabon yaki.

A cikin yini guda sojojin Rasha suka mamaye Kyiv da Kharav da Odessa, manyan biranen Ukuraniya. Suka karbe tekun Black Sea da tsibirin Snake Islands. Suka karbe filin jirgin sama na Hotsomel. Aka kashe mutum 137. Mil 20 ne kadai tsakanin inda sojin Rasha suke da Birnin Kyiv fadar shugaban kasar Ukuraniya.

Putin so yake ya hana Turai da Amurka su kafa masa sansani a kusa da kasarsa. Ba ruwansa da abin da zai biyo baya, ya shirya ya tare shi.

Bello Muhammad Sharada ya rubuto daga Kano

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet