Labarai
Kanywood: Ali Artwork ya angwance
A jiya juma’a aka daura auren fitaccen tauraron fina-finan Hausa Ali Muhammad Idris wanda aka fi sani da Ali Artwork da amaryarsa Hauw’u Muhammad Bello a birnin Kano.
An ɗaura auren Ali Artwork ko Madagwal ne bayan sallar juma’a a masallacin juma’a na Filin Kashu da ke yankin unguwa uku a ƙaramar hukumar Tarauni.
Ɗaurin auren ya samu halarcin wasu daga cikin jarumai a masana’antar Kanywood da sauran mutane daga ciki da wajen jihar Kano.
