Labarai
Kotu taki amincewa da bayar da belin DCP Abba Kyari
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar Litinin ta ki amincewa ta bayar da belin dakataccen Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, DCP Abba Kyari.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya ce kotun ta yanke hukuncin ne saboda wata damar da wata kotun tab a Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) damar tsare shi sama da kwana 14 domin ta samu damar kammala binciken da take yi a kansa.
Ana dai zargin Abba Kyarin ne da hannu a hada-hadar Hodar Iblis, wacce nauyinta ya kai kilogiram 25.
