Labarai
Sanata Rabi’u Kwankwaso da tawagarsa na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP
Jam’iyyar NNPP tabbatar da cewa suna kan tattaunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso akan batun komawar sa jam’iyyar kafin zaɓen shekarar 2023, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sakataren jam’iyyar mai barin Ambasada Agbo Gilbert Major ne ya bayyana haka a yau Talata a birnin tarayya Abuja.
Ya ce nan da ƴan kwanaki jam’iyyar ta NNPP za ta karɓi tsohon gwamnan da tawagar sa.
A cikin watan Fabrairu ne Sanata Kwankwaso ya jagorantar wani gagarumin taro na wasu manyan siyasar ƙasar nan ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna The National Movement TNM.
Tsohon gwamnan na jihar Kano, wanda dan jam’iyyar PDP ne, bai bayyana mukamin da yake son nema ba a wannan sabuwar ƙungiya ta siyasa.
Sai dai ana rade radin cewa zai fita daga jam’iyyar PDP sakamakon rashin jin dadin abubuwan da ke faruwa a cikinta.
