Labarai
An hana manema labarai shiga sauraron shari’ar Hanifah Abubakar
A yau Laraba wata babbar kotun jiha mai lamba 5 da ke zaman ta sakatariyar Audu Bako ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Usman Na’Abba, a cigaba da sauraron Shari’ar Abdulmalik Muhammad Tanko da kuma sauran mutanen da ake zargin su hannun wajen hallaka Hanifa.
Sai dai a zaman na wannan rana an hana ƴan jaridu shiga domin sauraron Shari’ar a sakamakon yadda wani jami’in daga hukumar tsaron farin kaya ta DSS zai bada shaida a gaban kotun amma kuma baya so yayi a gaban jama’a.
