Ilimi
Matsayar da aka cimma tsakanin ASUU da gwamnatin Najeriya
Kungiyar Malaman Jami’o’i a Najeriya ASUU ta ce, za ta koma wurin ƴaƴanta domin bayyana musu tattaunawar da suka yi da gwamnati da zummar janye yajin aikin da suke yi domin daukar matsayi akai.
Bayan kwashe sa’o’i kusan 8 suna tafka mahawara tsakanin shugabannin malaman da wakilan gwamnatin tarayya, rahotanni sun ce akwai alamun an fara fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.
Shugaban Kungiyar Malaman Farfesa Emmanuel Osodoke ya ce za su je su yi wa ‘ya’yan kungiyar bayani akan ganawar da suka yi kafin bayyana matsayin su ga jama’a.
A nashi bangare, Ministan Kwadago Dr. Chris Ngige ya ce bangarorin biyu sun cimma matsaya akan batutuwa da dama, kuma shugabannin malaman sun ce, za su je su gabatar da tayin da gwamnati ta musu domin janye yajin aikin.
Ngige ya ce, sun cimma matsaya akan batutuwa da dama, yayin da ma’aikatar ilimi ta kafa wani kwamiti domin Nazari akan sauran batutuwan da suka rage.
Ministan ya bayyana cewar gwamnati ta baiwa malaman akalla naira biliyan 92 daga cikin alawun su da suke bukata kamar yadda yarjejeniyar watan Disambar shekarar 2020.
