Connect with us

Featured

Kwankwaso da NNPP: Ko ina Akuya za ta da Kayan Taiki?

Da farko dai ina son in sanar da mai karatu, na jima ina faɗar cewa, bayan Buhari a halin da muke ciki, mutane biyu ne nake ganin cancantar su ta su jagoranci Arewa a fagen siyasa, Malam Nasiru el Rufa’i da Dr Rabiu Musa Kwankwaso.

Abin takaici tun kafin aje ko ina Malam Nasiru ya bayar da sanarwar baya da wata buƙata ta siyasa bayan ya bar muƙamin sa na gwamnan jihar Kaduna a shekara mai zuwa. Na biyu, yaƙi amincewa da ya buɗe ƙofar sa ga matasa domin su zauna da shi su nemi shawarar sa ko su kai masa koken su. Amma ina ganin Malam Nasiru inda zai amince ya ɗau girma, zai iya zama jagora ga matasan arewa koda ya bar harkokin siyasa. Sai dai wannan, wani maudu’i ne mai zaman kan sa).

Na biyu shi ne Dr Rabiu Musa Kwankwaso. A irin fahimtar da na yi masa, jagora ne nagari mai ƙoƙarin sauraron mutane da ɗaukar shawara, matuƙar shawarar za ta kawo cigaba da maslahar al’umma. Ga shi kuma yana kishin ganin ya baiwa matasa dama, wurin ganin sun samu makoma mai inganci a rayuwar su.

To amma fa duk da wannan Kwankwaso na da matsaloli irin na sa, Ɗan Adam tara ya ke bai cika goma ba. Babbar matsalar da yake fuskan ta ita ce kallafa ran sa da yayi akan lallai sai ya shugabanci ƙasar nan, abin takaicin kuma shi ne ya kasa gane cewa, hannu ɗaya baya ɗaukar jinka. Shi kaɗai ba zai iya kafa siyasa tayi tasiri a wajen jihar Kano ba. A ganina wannan shi be babban kuskure da RMK ya ke ƙoƙarin tafkawa a wannan zagon zaɓen da ke gabatowa.

Da farko dai ya sani, daga 1978 da aka fara yin siyasar ƙasa ba ta yanki ba. NPN ta yi nasara ne a dalilin haɗa karfi da ƙarfe da yawan manyan ƙasar nan suka yi ne. Inda ɗan takarar ta ya fito daga Arewa, mataimakin sa daga Gabas, shugaban jam’iyya daga yamma. Wannan ya sanya ta tsere sa’a. Ba kamar UPN da NPP da PRP da GNPP ba da kusan an kafa su ne akan sha’awar mutum guda, Awolowo, Zik, Malam Aminu da Waziri Ibrahim.

Ko a lokacin da Buhari ya fara gwagwarmayar siyasar sa, yayi yunƙurin kafa tasa jam’iyyar domin ya cimma burin sa na zama shugaban ƙasa, to amma ko da a Kano da yake da miliyoyin magoya baya siyasar tasa bata yi nasara ba. Saboda dai CPC an kafa tane domin sa, don haka takarar sa mutane suka damu da ita ba ta wani ba. Ba wanda ya fahimci illar siyasar takarar mutum ɗaya irin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Bayan ya tabbatar da jam’iyyar AD ta gama tashi daga aiki, sai ya fara ƙoƙarin kafa AC, ya kuma ƙoƙarin tabbatar da ya maida ta jam’iyyar, wannan shi ne dalilin da ya sanya bai taɓa yadda ya nemi takarar shugaban ƙasa a cikin ta ba. Ya baiwa babban ɓangaren da yafi kowanne adawa da bangaren sa dama, wato Arewacin Nigeria, inda ya tsayar da Atiku Abubakar a karon farko, ya kuma tsayar da Malam Nuhu Ribadu wanda duk basu yi nasara ba. Daga ƙarshe ya nemi haɗin guiwar manyan siyasun adawa na CPC da ANPP da kuma wani tsagi na PDP ya kafa APC. Wannan ya nuna irin kyakkyawar fahimtar da yayi wa siyasar Nigeria, domin kuwa a yau hakan sa ya cimma ruwa. An samu haɗakar dukkan ɓangarorin ƙasar nan, kuma da haka aka ka da PDP a zaɓen 2015.

Wata babbar matsalar da burin Kwankwaso zai fuskanta a zaɓe mai zuwa shi ne matsalar ɗaukan nauyi jam’iyya a jihohi 36 na ƙasar nan. Buɗe ofisoshi da ɗaukar nauyin su abu ne da ke buƙatar maƙudan kuɗaɗe musamman biyan albashi, hayar ofis, sayen motoci wanda wannan kawai na buƙatar sama da Naira Biliyan 5 daga nan zuwa zaɓe. A yadda na ga irin mutanen da Kwankwaso ke ƙoƙarin kafa jam’iyyar da su, a gaskiya ban ga wanda zai iya zuba wani jarin ku zo ku gani ba, a wannan tafiya ta sa ba.

Wani babban ƙalubalen na kuɗi shi ne, ɗaukar nauyin masu kula da zaɓe. Akwai rumfunan zabe guda 174,876 (Dubu Dari da Saba’in da Hudu da Dari Takwas da Saba’in da Shida). Ko da a ce a kowacce mutum biyu za ka ajiye ka biya shi N5000, kana buƙatar kusan Naira biliyan 2. Ban yi batun poster ba, bani batun kuɗin ayyukan yau da gobe ba. A ƙalla dai hidimar tsayawa takarar shugaban ƙasa a Nigeria na buƙatar ka kashe a ƙalla Naira Biliyan 6. Wannan kuma ba garanti ne na zaka ci zaɓe ba.

A shawarce ina ganin in har ya zama dole sai Kwankwaso ya ɗaukko sabuwar jam’iyya, to ya maida himma akan tsayar da ɗan takarar gwamna a Kano, wanda na tabbatar zai wuya a kayar da ɗan takarar sa. Alabashi, bayan shekara huɗu, ya fara ƙoƙarin ƙulla hulɗar siyasa da wasu jam’iyyu da za su iya haɗa guiwa su kayar da jam’iyya mai ci.

Amma maganar gaskiya a yanzu, ban ga mafita a wannan sabuwar jamiyya da Kwankwaso ya ɗakko ba. Ƙarshe dai za a raba kuri’ar Kano ne, kowa ya kwashi tasa. In kuma bai hankali ba, za a yi babun baɗilahu, shi bai samu shugaban ƙasa ba, ɗan takarar sa bai samu gwamna a Kano ba.

Fatuhu Mustapha ya rubuto daga Abuja – Najeriya

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet