Connect with us

Labarai

Yadda kashin farko na ƴan Najeriya su ka iso Abuja daga ƙasar Ukraine

A safiyar yau Juma’a ne kashin farko na ƴan Najeriya da aka kwashe daga birnin Bucharest na ƙasar Romania su ka sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke birnin tarayya Abuja.

Mutanen da a ka kwaso daga Ukraine sakamakon mamayar da Russia ta yi a ƙasar Ukraine sun nemi mafaka a ƙasar Romania.

Gwamnatin tarayya ta baiwa kamfanin Max Air da Air Peace kwangilar kwashe ƴan Najeriya da su ka maƙale a kan dala miliyan 8.5, bayan da a ka buƙaci su gudu zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Poland, Hungary, Romania da sauransu.

Yayin da Air Peace ba zai iya tashi daga Najeriya ba kamar yadda aka tsara, saboda wasu matsaloli, jirgin Max Air ya tashi daga Abuja zuwa Bucharest, a ranar Alhamis, kuma yanzu ya dawo da rukunin farko.

Jirgin mai lamba 747-400 mai lambar rijista 5N-HMM ya sauka a filin jirgin ne da karfe 06:11 na safiyar yau, kamar yadda wani jami’in kamfanin ya tabbatar wa wakilinmu.

Rahotanni sun baiyana cewa gwamnatin tarayya ta ba da dala 100 ga kowanne ɗan ƙasar da a ka dawo da shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet