Connect with us

Labarai

Hukumar KAROTA a Kano za ta bi kadin ma’aikacinta da ɗalibai su ka raunata

Hukumar kula da zirga-zirgar Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA, ta sha alwashin ɗaukar matakin shari’a a kan Ɗaliban Makarantar Sakandaren Dabo da ke unguwar Sabon Gari da ke yankin ƙaramar hukumar Fagge da ke jihar.

Hukumar ta bayyana haka ne a yau Talata ta bakin Kakakinta Nabilusi Abubakar Ƙofar Na’isa, lokacin da aka gabatarwa hukumar wasu ɓata-gari daga cikin Ɗaliban Makarantar Sakandaren Dabo, da ake zargi da nuna rashin ɗa’a ga Jami’an Hukumar KAROTA lokacin da suke gudanar da aiki a kusa da Makarantar.

Nabilusi Ƙofar Na’isa ya bayyana cewa sun sami nasarar cafke ɗaya daga cikin Ɗaliban Sakandaren Dabo mai suna Jabiru Suleiman Rimin Keɓe ɗan aji shida a makarantar mai shekaru 20 da haihuwa da yin amfani da Dutse wajen jifan Jami’an Hukumar Nura Baba Ali har ya samu rauni a fuskarsa.

Ɗaliban Sakandaren ta Dabo, sun jima suna kawo tsaiko da nuna rashin ɗa’a da hana kama masu laifi wanda hakan ya zama wajibi ga Hukumar ta ɗauki matakin Shari’a kan Ɗaliban domin gujewa ƙara samun rashin jituwa a tsakaninsu.

Ya ƙara da cewa wannan ba shi ne karon farko ba da Hukumar ke fuskantar rashin ɗa’a ga Ɗaliban Sakandaren don haka ya zama wajibi ga Hukumar ta ɗauki wannan matakin.

A ƙarshe, Hukumar ta ja hankalin Malaman Makarantar da iyayen Ɗaliban da su cigaba sa ido a kan ƴaƴansu domin sauke amanar da aka ɗora musu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet