Labarai
Idan Ba Ku: Yau ta ke ranar mata ta duniya
A duk ranar 8 ga watan Maris din kowace shekara ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Mata ta Duniya wadda kasashe da dama ke murnar zagayowarta.
An kebe wannan ranar ce a matsayin ranar tunawa da mata domin nuna mutuntawa da godiya da kuma kauna ga matan saboda gudunmuwar da suke bayarwa ga ci gaban al’umominsu ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa da ma siyasa.
Taken bikin na bana dai shi ne ‘Daidaiton jinsi a yau don ɗorewar gobe”.
Mata dai na fuskantar kalubale da dama a rayuwarsu, kama daga cin zarafi zuwa wariya da ake nuna musu musamman a ƙasashe masu tasowa.
A kan hakane aka kebe wannan rana domin wayar da kan matan sanin ‘yancinsu, da kuma nuna musu cewa su ma za a iya damawa da su a fannoni da dama na rayuwa.
A shekarar 1975 ne aka fara gudanar da bikin wannan rana.
Kiyasi dai ya nuna cewa, mata suke da kusan rabin adadin al’umar duniya, amma duk da haka, sukan gaza samun wakilcin da ya kamace su, musamman a fagen shugabanci, kamar yadda wani rahoton da cibiyar bincike ta Global Gender Gap ya nuna.
