Connect with us

Labarai

Ya kamata Buhari ya ɗaure ni da sauran ƴan siyasa saboda mun cuci Najeriya – Ibrahim Musa Kazaure

Tsohon Ministan Ayyuka, Ambasada Ibrahim Musa Kazaure ya ce ya kamata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kama shi da sauran ƴan siyasa da su ka rike madafun iko a ɗaure su sabo da sun zalunci ƙasar nan.

Da a ke zanta wa da shi a wani shiri a tashar rediyo ta Radio France International, Kazaure ya ce duk ƴan siyasar Najeriya ɗaya su ke, inda ya ce babu wani wanda ya ke yi don talakawa.

A cewar sa, ya faɗa wa Shugaba Buhari da ya kame duk ƴan siyasar da su ka wawashe kuɗaɗen gwamnati har da shi.

Tsohon Ministan ya ce duk ƴan siyasan da su ka rike madafun iko tun daga 1999 ba su yi wa ƙasar komai ba.

“Har ni da na ke wannan maganar, ya kamata a ɗaure mu sabo da ba mu yi wa ƙasar nan komai ba

“Na sha faɗin cewa ni Ibrahim Musa Kazaure, mun zalunci Najeriya da talakawan ta.

“Magana ta gaskiya ita ce, dukkan mu kanwar ja ce. Abin da mu ka yi wa Najeriya ba haka ya dace mu yi mata ba sabo da wasu daga cikin mu sun samu dama wasu kuma basu samu ba.

“Ni dai gaskiya na faɗa. Dukkkan mu da mu ka yi sata, a matsemu mu dawo da kuɗaɗen da mu ka sata. Na faɗawa Buhari, a kame mu a ɗaure mu har sai mun dawo da kuɗaɗen da mu ka sata.

“Ni ba zan sake karɓar wani muƙami a kasar nan ba, ko da kyauta ne,” in ji Kazaure.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet