Connect with us

Labarai

Najeriya na buƙatar Khalifa Sanusi II da Moghalu a matsayin shugaba da mataimaki – Bello Sharada

Fitaccen mai yin sharhi akan al’amuran yau da kullum musamman siyasar jihar Kano da Najeriya, Bello Muhammad Sharada ya bayyana cewa Najeriya tana buƙatar tsohon shugaban babban bankin Najeriya kuma tsohon Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II da tsohon mataimakin bankin CBN Farfesa Kingsley Moghalu a matsayin shugaban ƙasa da mataimaki.

Bello Sharada, wanda ɗan Jami’yyar APC ne ɓangaren Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a yammacin yau Litinin.

Sharaɗa, ya ce “IDAN aka cire maganar siyasa, wato ina nufin babu maganar yanki ko ƙabila ko addini a wannan yanayin, a yau, a ƙasar nan, mutum biyu da suka jagoranci Babban Bankin Najeriya sun da ce a basu ragamar Najeriya a 2023”.

“Na farko: Halifa Muhammad Sanusi II a matsayin shugaban kasa. Na biyu: Farfesa Kingsley Moghalu a matsayin mataimakin shugaban ƙasa”. In ji Bello Sharaɗa.

Khalifa Muhammadu Sanusi II tsohon ma’aikacin banki ne kuma gogaggen masanin tattalin arziƙi wanda ƙwarewarsa a aikin banki da tattalin arziki ta sa gwamnatin Marigayi Malam Umaru Musa Ƴar Adua ta naɗa shi gwamnan babban bankin Najeriya.

Shi kuwa Farfesa Kingsley Moghalu, fitaccen lauya ne kuma masanin tattalin arziki, shi ne tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar Young Progressives Party wato YPP a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019, wanda daga baya ya bar jam’iyyarsa ta YPP a watan Oktoban shekarar 2019 kuma a cikin kwanan nan ya shiga jam’iyyar ADC.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet