Labarai
Tsohon Maitaimakin Gwamnan jihar Adamawa ya fice daga APC zuwa jam’iyyar NNPP
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Adamawa, Sa’ad Tahir, ya fice daga Jami’yar APC zuwa NNPP.
Tahir ya sanar da sauya shekar ta sa ne a wani taron manema labarai a Yola a yau Talata.
Sa’ad Tahir dai ya taɓa zama Mataimakin Gwamna a lokacin Mista Bala James Ngilari yana mulkin jihar a shekarar 2014 a jam’iyar PDP.
Haka kuma a shekarar 2018, Tahir ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC inda ya kasance a cikin har zuwa yau da ya sanar da ficewar sa da ga cikin jam’iyar.
Ya ce ɗaya da ga cikin dalilan da su ka sanya ya ɗau wannan matakin shi ne domin ya kare martabar dimokuraɗiyyar ƙasar nan.
