Connect with us

Labarai

Satar Taliya da Indomie ta sanya wani Ɗalibi samun gurbin zama a gidan yari

Wata kotu a yankin Gwagwalada da ke birnin tarayya Abuja, a yau Alhamis, ta yankewa wani ɗalibi mai suna Hilary Yunana, ɗan shekara 19 hukuncin wata huɗu a gidan yari sakamakon satar taliya da kuma indomie a wani kanti.

An tuhumi Yunana, mazaunin ƙauyen Bassa a kan hanyar filin jirgin sama, da laifin karya kofar gida da sata.

Da ya je yanke hukunci, alƙalin kotun, Sani Umar, ya aika Yunana gidan yarin duk da ya amsa laifin sa ya kuma nemi kotun da ta yi masa sassauci.

Sai dai kuma alƙalin ya baiwa matashin zaɓin tarar naira dubu 10 ko kuma ya yi watanni biyu-biyu a kowanne laifi guda biyun.

Alƙalin ya ce hukuncin darasi ne ga duk wani wanda ya ke son bin irin wannan mummunar hanyar.

Tun da fari, mai ƙara, Abdullahi Tanko ya shaida wa kotu cewa mai laifin ya ɓalle shagon wata Gift Ogochukwu da su ke unguwar ɗaya a ranar 4 ga watan Maris.

Ya ce bayan ya fasa shagon, ya sace taliya leda 7 da i domie leda 5 da kuma kuɗi Naira dubu 10, gaba daya dai dubu 13 kenan.

Ya ce laifukan sun sabawa sashe na 346 da 287 na kundin dokar Penal Code.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet