Connect with us

Labarai

Gwamnatin Ganduje na shirye-shiryen kama Bashir Hayatu Jantile

Jami’an tsaron ƴan sanda a jihar Kano na shirye-shiryen kama Alhaji Bashir Hayatu Jantile (Gentile), mataimaki na musamman ga shugaban majalisar dattijawan Najeriya, saboda sukar manufofin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

Bashir Hayatu Jantile, wanda mai sharhi ne a kan al’amurran yau da kullum ne, kuma makusanci ga tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau, ya kan soki yadda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ke tafiyar da gwamnati a cikin shirye-shiryen siyasa da ake gabatarwa a Kano.

A ɗan lokacin nan dai masu adawa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kafar rediyo na fuskantar kamu daga jami’an tsaro inda akan gurfanar da su a gaban mai shari’a Aminu Gabari da ake masa zargin karɓar cin hanci da rashawa.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa tun da farko jami’an ƴan sandan sun shirya kama Jantile ne sai dai shirin hakan bai kai ga nasara ba, inda daga bisani aka gayyace shi domin ya amsa wasu tuhume – tuhume da aka gabatar musu.

Sai dai kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ba shi da masaniya akan batun. Ya ƙara da cewa amma zai yi bincike domin tabbatar da faruwar lamarin.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Janairun shekarar nan ne ƴan sanda su ka kama tsohon Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano, Mu’azu Magaji.

Mu’azu Magaji, wanda ake yi wa lakabi da Ɗan Sarauniya, ya yi fice wajen sukar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje a shafin Facebook.

Hakazalika a dai cikin watan nan na Maris da mu ke ciki kotun Majistire ƙarƙashin Aminu Gabari ta aike da Abdulmajid Danbilki Kwamanda, wanda ɗaya ne daga cikin jiga-jigan APC a jihar a gidan yari.

Gwamnatin Kano ta gurfanar da Danbilki Kwamanda ne bisa zargin batawa gwamnati suna da kuma tunzura al’umma.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet