Connect with us

Labarai

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji masu yawa bayan hari kan jirgin ƙasa a hanyar Abuja – Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa an sace wasu fasinjoji da ba a bayyana adadinsu ba daga wani jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a yammacin ranar Litinin.

Shaidu sun ce jirgin ya kauce daga kan hanyarsa bayan fashewar wani abu a kan hanyarsa.

Rahotanin sun ce an samu asarar rayuka yayin da wasu da dama suka jikkata.

An kai wa jirgin kasan mai dauke da fasinjoji kusan 1,000, harin ne da misalin karfe 8 na dare.

Fasinjoji da kuma ‘yan uwan wasu fasinjojin sun bayyana cewa lamarin ya yi matukar muni kuma har yazu ba a san takamaiman mutanen da lamarin ya shafa ba.

Wani fasinja ya ce bayan jirgin ya tsaya, ƴan bindigar sun kewaye shi tare da bude wuta.

Mutane sun sunkuya kasa domin samun mafaka kuma daga nan ne maharan suka nufi hanyar jirgin, inda suka harbe fasinja ɗaya a kusa da inda suka yi awon gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba, in ji shi.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar ya ce an tura sojoji domin ceto fasinjojin tare da kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.

Yawaitar kai hare-hare da sace-sacen mutane da ake yi a babban titin Abuja da Kaduna ce ta sa matafiya da yawa suka gwammace yin tafiya ta jirgin kasa.

Sai dai wannan shi ne karo na biyu da ake kai hari kan hanyar jirgin cikin watanni shida da suka wuce.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet