Connect with us

Labarai

NNPP ta zaɓi Farfesa Rufa’i Alkali a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa

Jam’iyyar adawa ta New Nigeria Peoples Party, NNPP, mai alamar kayan marmari, ta yi babban taron ta na ƙasa a jiya Laraba a Abuja, inda ta zaɓi Farfesa Rufai Alkali a matsayin shugaban jami’yar na ƙasa.

Jam’iyyar ta zaɓi shugabannin na ta guda 30 gaba ɗayansu ta hanyar maslaha.

Wasu daga cikin shugabannin sun haɗa da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Rufai Alkali daga Jihar Gombe; Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa , AVM John Ifemeje mai ritaya (Anambra); Sakataren Jam’iyya, Dipo Olayoku (Ogun) da kuma Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa, Suleiman Hunkuyi Kaduna).

Sauran sun haɗa da Mataimakin Sakataren Jam’iyya na Ƙasa, Ahmed Ajuji, (Adamawa); Ma’ajin Jam’iya na Ƙasa; Sanin Malam (Bauchi); Lauyan Jam’iya , Bem Angwe (Benue), da dai sauransu.

Da ya ke jawabi bayan ya zama Shugaban jam’iyyar, Alkali ya ce kafa jam’iyar wani tushe ne na samar da sabuwar Nijeriya.

A cewar sa, NNPP za ta yi iya kokarinta ta tabbatar da ci gaban Najeriya da ga ko wanne ɓangare.

“Ƴan Najeriya sun gaji kuma yanzu mafita su ke nema. To mu ne mafita kuma za mu yi iya bakin ƙoƙarin mu mu ga cewa an tafi da kowa,” in ji shi

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet