Labarai
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya tsallake rijiya da baya a wani haɗarin mota
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya tsallake rijiya da baya a wani haɗarin mota da ya rutsa da tawagarsa akan hanyarsa ta zuwa gida daga filin jirgin sama na Abuja.
Lamarin ya faru ne a yammacin yau Laraba a lokacin da Jonathan ɗin wanda jakada ne na musamman a ƙungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, wato ECOWAS, ya ke dawowa daga filin tashi da saukar jiragen sama da ke Abuja zuwa gidansa.
Haɗarin dai ya yi sanadiyyar rasuwar hadiman Jonathan guda biyu.
Sai dai a lokacin haɗa wannan rahoton wata majiya ta tabbatar da cewa tsohon shugaba Jonathan ɗin na gidansa cikin ƙoshin lafiya.
Ana yawan samun hadarin mota a Najeriya saboda rashin hanyoyin masu kyau da kuma tukin ganganci.
