Connect with us

Siyasa

Ƙungiya- Za mu gurfanar da Hamza Almustapha a kotu matuƙar ya ƙi fitowa takarar shugaban Ƙasa

Ƙungiyar masu rajin kasancewar Manjo Hamza Almustapha ya zama shugaban Najeriya a zaɓen baɗi da ke ƙaratowa, watau Hamza Almustapha Awareness shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, ta sha alwashin gurfanar da Almustaphan a gaban ƙuliya matuƙar bai amince da buƙatarsu ta tsayawa takara ba.

Shugaban ƙungiyar Malam Salisu Mu’azu Rijiyar Zaki, ne ya bayyana hakan yau Lahadi yayin taron da ƙungiyar ta gudanar a cibiyar nazarin harkokin dimukuraɗiyya da ke Gidan Mambayya a jihar Kano.

Malam Salisu Mu’azu ya ce, “Dalilin gudanar da shi a gaban kotun shi ne, matuƙar bai tsaya takarar ba ta tabbata cewa baya kishin halin ƙunci da ƴan Najeriya ke ciki.”

Haka kuma ya ƙara da cewa, “A halin da Najeriya da al’ummar cikinta suka faɗa na matsalolin tsadar rayuwa, taɓarɓarewar harkokin tsaro da sauran matsaloli da dama, muna ganin cewa babu wanda zai iya dawo da Najeriya cikin hayyacinta sai shi.”

“kusan duk wanda ya san lokacin da shugaban ƙasa na mulkin soji Janar Sani Abacha ya yi mulki, ya san irin gwagwarmaya da gudunmawar da Dr Hamza Almustapha ya yi wajen tabbatuwar zaman lafiya da cigaban Najeriya wanda har sai da ta kai marigayi Abacha ya tura shi ƙasashen duniya domin nemo wa Najeriya hanyoyi da kuma ababen ci gaba da dama.”

Babu wata jam’iyya da muka zaɓa da zai yi takara a cikinta kasancewar bai ma san muna yin wannan taro ba, illa kawai mu mun san cewa shi ne ya cancanta don haka muka fito domin nuna masa goyon bayanmu.” inji Salisu Mu’azu

Ya ƙara da cewa a baya ƴan Najeriya sun ga mulkin Power, wanda bai haifar mana da ɗa mai ido ba, kwatsam sai ƴan Najeriya suka zaɓi mulkin Canji wanda ya fi na Power muni.

A nasa ɓangaren, Malam Shariff Sidi Abba Abubakar, Hayya-Kallah, ya ce,”Mun taru ne domin neman Almustapha ya fito tara la’akari da irin nagartarsa bisa tawassali da gudunmawarsa ga Najeriya.”

Haka kuma ya ƙara da cewa a hasashensa, “Matuƙar ya zama shugaban Najeriya zai daƙile matsalolin tsaro tare da magance irin rikice-rikicen da ake fama da su tsakanin shiyyoyin Najeriya.

Malam Shariff Sidi, ya ƙara da cewa, ko a lokacin mulkin soja Manjo Almustapha ya bada gudunmawa matuƙar, sai ga shi yanzu kuma ya zama ɗan siyasa don haka yana kyautata zaton cewa zai bada gudunmawar da ma ta fi ta baya.

Shi ma Malam Lawan Ali Beli guda cikin masu goyon bayan Manjo Almustapha, cewa, ya yi “Ko da ganin irin yadda al’umma suka yi cikar kwari a ɗakin taron, ya isa ya nuna cewa lallai ƴan Najeriya na fatan kasancewarsa shugaban tarayyar Najeriya kuma hakan zai taimaka matuƙar wajen magance tarin matsaloli.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantmatbetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibomsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet