Featured
Me ku ka taɓa yi don ganin an kawo ƙarshen almajiranci (I)?
Ko kuma dai kuna layin masu harbin iska kan batun almajiranci a yanar gizo?
A tunanin ku wannan ita ce mafitar? Sam! Abin ba haka yake ba Surutu da cece-ku-ce a dandalin sada zumunta ba shi zai kawo ƙarshen matsalar ba, saboda mafiya akasarin waɗanda ke hangaɗo yaransu zuwa wannan tsari, ba sa tare da mu a wannan kafar, suna can a ƙauyukan su, amma duk da haka bana goyon bayan yadda suke saƙo yaran haka sakaka, ba tare da wani daidaitaccen tsari ba. Karatun allo abu ne mai ƙyau, tsarin da ake bi ne ya samu tasgaro.
Zuwa Almajiran ba shi ne aibu ba, gararambar da yaran suke yi cikin ƙasƙanci suna ga ludaya da barace-baracen akan titi shi ne aibun.
Domin a wannan tafarkin ne su ke cin karo da ɗumbin ƙaluban na rayuwa tun basu san mece ce rayuwar ba, siraɗi ne mai wahala amma a haka za su saba har zuƙatansu wasunsu su ƙeƙashe.
Ƙalilan da ga cikinsu ne za su yi kuskure sai ayi musu jam’u, saboda ana ganin kamar ba su da galihu, su ba mutanen kwarai ba ne. Wannan shi ke ba ɓata gari damar shiga rigarsu su aikata ɓarna sai a fake da guzuma a harbi karsana.
Yaran nan su ma ba haka suka so su tashi cikin al’umma a matsayin jinsin mutanen da ake ƙyara ba.
Haka suka ɓudi ido suka ga ni :
Iyayen su sun turo su, ba tare da samar mu su ababen buƙata ba.
Malaman su sun karɓe su ba tare da tsara wasu ƙa’idoji ba.
Gwamnatin ta bar su kara zube, ba tare da shimfiɗa wata doka ba.
Mafi muni abin da ya fi taɓa mu su zuciya shi ne ƙyara daga gare mu, ƙwarai! Mu al’umma ba, ba mu ɗauke su a matsayin mutane ba, babu tausayawa da nuna jin ƙai a gare su, sai surutun tsiya ba tare da aikata wani abu da zai canza rayuwar su ba.
Idan cece-ku-ce za a ci gaba da yi to ba a ɗakko hanyar gyara ba, sam! Matsalar ba za ta gyaru a haka ba sai ma dai ta ƙara taɓarbarewa.
Gyara tsarin karatun allo ba aikin ɓangaren ɗaya ba ne, dole sai Gwamnati ta shiga, iyaye sun gyara, malamai sun dai-dai, ƙungiyoyi masu zaman kansu sun ɗaga murya, al’umma kuma sun taimaka, sannan za a iya samu fiye da abin da ake so.
Kyakkyawan misalin shi ne wannan hoton da yake ƙasa, Yaron da kuke gani a tare da ni alma’jiri ne amma kulawar da ya ke samu ta ɓangaren ilimin ba kowani ɗa ne zai iya samun kamarsa ba, sai wanda Ubansa ya isa wallahi.
Wannan wani kyakkyawan aikin jin kai ne na Kungiyar da na ke aiki a ƙarƙashin ta HUMANITY FOR ALL Wanda ta ragamar canza rayuwar yaran nan. Fisabillahi.
Abin da ya kamata al’umma mu assasa kenan, ba surutu ba.
Yawwa daga ƙarshen duk wanda ya karanta ya fahimta to Madallah.
Wanda kuma ya karanta bai fahimta ba shi ma Madallah.
Amma fa kar wanda ya kuskure ya kira ni da ‘yar aiken yahudawa. Don nasan ƙarshen zancen ke nan.
Zan dawo a wallafa ta gaba insha Allah, ba dogon rubutu ba ne tarin hujjoji ne da za ku gwangwaje idanun ku da su.
Hauwa Shehu ta rubuto daga Kano – Najeriya
