Labarai
Buhari ya sha alwashin hana masu maguɗin zaɓe sakat a 2023
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin yin magudin zabe a 2023 da su guji yin hakan yana mai shan alwashin hana su sakat.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis da daddare yayin da ya shirya buda-baki ga jakadun kasashen waje da ke aiki a Najeriya.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ya fitar ta ambato Shugaba Buhari yana cewa “ya kamata wadanda suke shirin yin magudin zabe a zabuka masu zuwa su sake tunani saboda na sha alwashin kare martabar al’ummar Najeriya a yayin da suke kada kuri’unsu.”
Kazalika Shugaba Buhari ya gargadi kasashen waje da su guji yin katsalandan a zabukan kasar da ke tafe.
