Connect with us

Siyasa

Masu ruwa da tsaki sun bai wa Hafizu Kawu fiye da miliyan 20 don sayen fom ɗin sake tsayawa takara

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Tarauni Hafizu Ibrahim Kawu, ya bayyana farin cikinsa bisa bayan da ya karɓi fiye da naira miliyan 20 domin sayen fom ɗin sake tsayawa takara daga masu ruwa da tsaki da kuma wasu ƙungiyoyi.

Ƙungiyoyin da suka bada tallafin sun haɗa da ƙungiyoyin ƴan kasuwa da na ɗalibai da kuma waɗanda suka ci gajiyar ayyukan ɗan majalisar da shugabannin jam’iyyar APC sai manyan jami’an gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomin biyu da sauransu.

Ɗan majalisar ya yi Alkawarin cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba, wajen ci gaba da gudanar da ayyuka masu nagarta domin ƙarfafa gwiwa ga wadanda suka yi masa wannan tagomashi da kuma samarwa al’umma sauƙi.

Da yake jawabi a madadin masu ruwa da tsaki, babban mai taimakawa gwamnan Kano kan harkokin siyasa, Alhaji Mustapha Mai Hula, ya ce bada tallafin ya zama dole domin Hafizu Kawu ya ci gaba da samar da ci gaba da ba a taɓa ganin irinta ba a mazabar.

“Mun san cewa yana da kuɗin sayen fom ɗin tsayawa takarar, amma ba za mu bar shi ya saya da kansa ba.

Mun tara kuɗin ne ta hanyar bayar da gudunmawar naira dubu goma-goma a lokuta mabambanta”.

Mai Hula ya kuma bayyana cewa Hafiz Kawu ya canza salo da rayuwar jama’a da dama ba wai a mazabar sa ta tarayya kadai ba, harda Jihar Kano baki daya.

Dan majalisar wanda zai sake tsayawa takara a karo na biyu, ya bada tabbacin cewa zai kara yin kokari fiye da wannan lokacin matukar ya koma majalisar ta hanyar samar da ababen more rayuwa da inganta rayuwar jama’a tare da ci gaba da inganta abubuwan da aka cimma kawo wannan lokacin.

“Manufata ita ce ci gaba da samar da ayyukan ababen more rayuwa da bunkasa jarin al’umma tare da ci gaba da inganta ayyukan da muka yi a cikin shekarun da suka gabata wadanda suka ba wa ‘yan mazabarmu karfin gwiwa, har ta kai ga tara wannan kudi don tallafa mana kawai don ci gaba da kuma tabbatar da cewa mun ci gaba yin wakilci mafi kyau.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzasweet bonanzapadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabetTürkiyenin Casino Sitelerivdcasinograndpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetsahabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet