Connect with us

Labarai

INEC ga jam’iyyu: Ba za mu ƙara wa’adin zaɓen fidda gwani ba

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta ce ta bada wa’adin gudanar da zaɓukan fitar da ƴan takarar zuwa ranar Juma’a 3 ga watan Yuni mai kamawa.

Hukumar ta kuma ce, jam’iyyu na da “Wata guda daga yau” don kammala zaɓen fidda gwanin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, INEC ta ce dukkanin jam’iyyun siyasa 18 sun ba da sanarwar da ake buƙata da ke nuna ranakun gudanar da babban taronsu, da zaɓukan fitar da ƴan takara a muƙamai daban-daban, har ma da saura shirye-shiryensu.

Festus Okoye, shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, ya ce a miƙa sunayen ƴan takarar shugaban kasa da na ƴan majalisun tarayya tsakanin ranakun 10 zuwa 17 ga watan Yuni yayin da na gwamnoni da na majalisun jihohi ya kasance tsakanin 1 zuwa 15 ga watan Yuli.

“Idan za a iya tunawa a ranar 26 ga Fabrairun da ya gabata ne hukumar ta fitar da jadawalin yadda babban zaɓen baɗi zai gudana, inda a ciki ya tanadi lokacin da jam’iyyu za su gudanar da zaɓen fidda ƴan takara daga ranar 4 ga Afrilu zuwa 3 ga Yunin bana, ” in ji sanarwar.

“A bisa dokar sashe na 82 (1) na dokar zabe da aka yiwa gyara a bana, dukkanin jam’iyyun siyasa 18 sun ba da sanarwar da ake buƙata da ke nuna ranakun gudanar da babban taronsu da na ƴan majalisun tarayya da nufin tantance ƴan takara a mukamai daban-daban na zaɓe kamar yadda kundin tsarin mulki ya kayyade da kuma dokar zabe.
“Za a gabatar da sunayen ƴan takarar shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya ta kafar Internet ɗin hukumar INEC daga ranar 10 zuwa 17 ga watan Yuni na bana, yayin da za a gabatar da na ƴan takarar gwamna da na ‘yan majalisar jiha tsakanin 1 ga Yuli zuwa 15 ga Yulin bana.

“Ana kara tunatar da jam’iyyun siyasa cewa dole ne su miƙa wa hukumar jerin sunayen ƴan takarar da ya kamata su tsaya.”

Hukumar ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da jam’iyyu domin tabbatar da bin ƙa’idojin da aka gindaya na dukkan ayyukan zaɓen na baɗi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet