Featured
Takarar shugaban ƙasar gwamnoni masu ci: A ɗauri kashi ko a ɓata igiya?
Daga nan zuwa a yi zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa a PDP da APC, Allah na gani ina tausayawa lalitar jihohin Sokoto, Bauchi, Kogi, Ekiti da Ebonyi. Abinda ya sa ban ambaci jihar Rivers ba, ita jiha ce mai arziƙi kuma ƙarshen ta ma mai daskararriyar muryar nan har sibaren ɗanyen man fetur yana taɓawa yana samun ƙazaman kuɗaɗe.
Tsakani da Allah dubi yadda gwamnonin Sokoto da Bauchi suka shafe tsahon lokaci suna karaɗe jihohin ƙasar nan a jirgi na musamman (Private Jet) da sunan masalaha (Consensus) har zuwa sanda tafiyar ta tarwatse. Allah ne kaɗai ya san yawan kuɗaɗen da suka kashe a wannan yawon ga shi kuma kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba. Yanzu kuma kowannen su ya ƙara bazama jihohi da sunan ganawa da wakilai (Delegates) kuma kamar yadda kowa ya sani a al’adar siyasar Najeriya, duk inda aka je wannan ziyarar fa sai an ajiyewa wakilan nan (Delegates) da shugabannin jam’iyya da masu faɗa aji kamar shugabannin gargajiya da na addini da ake ziyara wani dunƙuli mai kauri.
Akwai takaici matuƙa a ce jihohi irin su Kogi da ko albashi gwamna ba ya iya biya yadda ya kamata amma a ce ya jefa kan sa da dukiyar al’ummar da ke a matsayin amana a hannunsa a wannan bulunbituwar ta takarar shugaban kasa. Haka kawai ayi ta ɗiban dukiyar jama’a ana baiwa ƴan nanayen da duk cikin su ba wanda yake da ƙima ko martabar da zai sa ko da mutum ɗari ne su zaɓe ka.
Babban asara kuma ga irin waɗannan jihohin tana tafe a ranar da jam’iyyun za su yi zaɓen fidda gwanin. Wannan ce ranar da iya kashe kuɗin ɗan takara, iya shagalinsa saboda haka dukkan ɗan takara zai ƙure malejin kashe kudin sa don ganin ya cimma nasara a wannan ranar. Wannan ranar ne kuma jikin lalitar jihohin da gwamnonin su ke takarar shugaban ƙasa za ta gaya musu sosai.
An ce ido ba mudu ba, amma ya san ƙima. Mafi yawan gwamnonin nan adashin asara kawai suke zubawa jihohin su a takarar shugaban ƙasar nan domin kuwa zai yi mutuƙar wahala a ce ɗaya daga cikinsu ya kai ga nasara. Kamar yadda Sani Danja ke fada a wata wakarsa “Sama ta yiwa yaro nisa, sai dai ya tada kai yai kallo”, kuma ina tunanin su ma kansu gwamnonin sun san da hakan. Amma da ya ke ba kuɗaɗen su ne su ke zubawa ba, wannan ya sa suke ganin ba su da asara ko nawa su ka kashe a takarar da suka san ba su da nasara.
Ban da mai girma Madugu namu na gargajiya, ba wani tsohon gwamna da ya taɓa yin takara yana mulki da ya sake gwadawa bayan ya sauka. Shi ma kuma ga shi dai sai hakura yayi zai ɗebi ruwansa daidai tsaki a ƙaramar jam’iyya domin ya san ba shi da kumbar da zai yi su sa da ita a babbar jam’iyya.
Bayan kuɗaɗen jihohin da ake sabautawa a lokacin neman takarar nan, haka kuma ayyukan cigaban jama’a da kula da rayuwar su ke tsayawa cik a irin waɗannan jihohin saboda Gwamna ba ya nan. Jami’an gwamnati ma masu son zuciya su ma kakarsu ta yanke saƙa sai su yi son zuciyar su yadda suke so saboda ba tsayayyen shugabancin da zai sa mu su ido.
Abin takaici a ɗaya hannun kuma, su kansu naɗaɗɗun shugabanni a gwamnatin tarayya da ke takara a matakai daban-daban su ma sun yi mursisi sun ƙi sauka daga mukamansu duk kuwa da dokar da ta tilasta masu yin haka. Shi ma kuma shugaban ƙasa ya zuba musu ido suna ta amfani da dukiyoyi da alfarmar ofisoshinsu suna neman biyan buƙatunsu na kashin kansu. Wannan fa shi ne ma’anar kwarafshin da duniya ta yadda da ita, kuma bai kamata a ce mai girma shugaba Buhari ya kau da kai ko kuma ya ba da goyon baya hakan na faruwa ba.
A ƙarshe ya kamata talakawa mu san cewa wajibin mu ne mu tashi mu ga cewa an gyara wannan tsarin na siyasa a Najeriya domin kuwa ba yadda za a yi su shugabannin siyasar da tsarin ke amfanar da su a ce su ne za su gyara. Muna yaudarar kan mu ne in muka cigaba da tunanin cewar wannan siyasar da ake yi mai ɗan karen tsada ce za ta fitar mana da shugabanni nagari da za su inganta rayuwar mu. In dai aka cigaba da wannan tafiyar, sai dai mutane su cigaba da zuba jarin dukiyar su wajen neman mulki don su kwashi riba ba don su kyautata rayuwar jama’a ba.
Isah Mansur ya rubuto daga Kano – Najeriya
